Tinubu ya koma Najeriya bayan hutun mako biyar a Paris

Tinubu Returns 2
Tinubu Returns 2

Zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan wata ziyara da ya kai ƙasar Faransa inda ya shafe tsawon mako biyar.

Tinubu ya sauka ne da yammacin Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja babban birninTarayyar.

Wani bidiyo da Bayo Onanuga mataimaki na musamman ga zaɓaɓɓen shugaban ya wallafa a shafinsa na Tuwita ya nuna manyan jiga-jigai da makusantan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na yi masa maraba.

Daga cikin waɗanda suka halarci tarbar Tinubun, har da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban, Kashim Shettima da Simon Lalong, babban daraktan rusasshen kwamitin yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu na dakon saukar sa a filin jirgin sama.

Cincirindon ‘ya’yan jam’iyya mai mulki wato APC da magoya bayan Tinubu ne suka tarbe shi lokacin da ya sauka a filin jirgin sama da yammacin Litinin.

An yi ta raɗe-raɗi da yaɗa jita-jita game da tafiyar tasa zuwa Paris, inda wasu suka riƙa cewa ganin likita ya tafi, saboda taɓarɓarewar lafiyarsa.

Komawarsa gida Najeriya ta kawo ƙarshen duk irin waɗannan raɗe-raɗi da jita-jita.

Kuma a yanzu saura kwana 35 a rantsar da Bola Ahmed Tinubu matsayin shugaban Najeriya, inda zai karɓi ragamar mulki ranar 29 ga watan Mayu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here