Gwamna Mohammed ya kafa dokar hana fita a Bauchi

Bala Mohammed new 678x381 1
Bala Mohammed new 678x381 1

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya sanya dokar hana fita a garin Gudum Hausawa da ke wajen birnin Bauchi a Larabar makon nan.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Malam Mukhtar Gidado, ya fitar.

A cewarsa, ɗaukar matakin ya biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin al’umma inda mutane uku suka rasa rayukansu, da dama suka jikkata tare da ƙona wasu gidaje.

Giɗaɗo ya kuma ce, gwamnan ya sanar da jama’a cewa tuni jami’an tsaro suka cafke waɗanda ake zargi da haddasa rikicin.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro ba ga dukkanin al’ummomin jihar.

“Mai girma gwamna ya kuma umarci jami’an tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin faruwar lamarin tare da yin Alla-wadai da kone-konen gidaje da sauran kadarori da ɓata garin da ba a san ko su wanene ba suka yi.

“Gwamnan wanda ya kuma bayar da umarnin girke jami’an ƴan sanda a yankin a wani mataki na tabbatar da tsaro, ya kuma bukaci al’ummar yankin da su zauna lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabilanci ba domin babu wata al’umma da za ta ci gaba ba tare da an samu zaman lafiya a cikinta ba,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here