Tinubu ya amince da sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Kano zuwa jami’ar Yusuf Maitama Sule

tinubu 2

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya canza sunan Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Kano zuwa Jami’ar Ilimi ta Yusuf Maitama Sule.

Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan bayanai da dabaru ya fitar a ranar Litinin, ta ce Tinubu ya yi na’am da cewa ambatar sunan Yusuf Maitama Sule zai zaburar da matasa masu tasowa don tabbatar da gaskiya da kishin kasa.

Jami’ar Ilimi ta tarayya da ke Kano na daya daga cikin manyan jami’o’in ilimi guda bakwai a karkashin gwamnatin tarayya.

A matsayinta na jami’ar ilimi ta tarayya, za ta ci gaba da taka rawar gani wajen horar da malamai, da kara karfafa fannin ilimi a Najeriya.

SolaceBase ta ruwaito cewa Alhaji Maitama Sule da aka haifa daga shekarar 1929-2017, ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar Nijeriya a tsawon rayuwarsa.

Ya yi aiki a matsayin wakilin Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya a New York, inda ya kasance shugaban kwamiti na musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan Yaki da wariyar launin fata.

Ya kuma yi aiki a matsayin babban mai shari’a na majalisar Wakilai ta tarayya (1954-1959), Jagoran tawagar Najeriya zuwa taron kasashe masu zaman Kansu (1960), kuma Kwamishinan karbar Korafe-korafen Jama’a na tarayya na Farko (1976) kana Ministan Ma’adinai da Makamashi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here