Dalhatu ya doke dan Abacha, ya samu tikitin gwamnan PDP a Kano

Mohammed Abacha 750x430 1
Mohammed Abacha 750x430 1

Muhammad Sani Abacha, da ga tsohon shugaban mulkin soja, marigayi Janar Sani Abacha, ya sha kaye a zaben fidda gwanin gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Kano.

SolaceBase ta ruwaito cewa Muhammad Bello Dalhatu ya doke shi, inda ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa a jihar.

Da yake sanar da sakamakon, shugaban Kwamitin Zaben Fidda Gwanin Gwamnan PDP a Jihar Kano, Umar Danjani Hadejia ya ce zaben ya gudana cikin lumana kuma an gudanar da shi bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da ka’idodin zabe.

Ya bayyana cewa Abacha ya samu kuri’u 749, yayin da Dalhatu ya samu kuri’u 2,233 inda ya lashe zaben.

“Bayan samun mafi yawan kuri’u masu inganci da aka kada, ina sanar da Alhaji Muhammad Bello Dalhatu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna na PDP a Jihar Kano kamar yadda doka ta yi tanadi,” in ji Hadejia.

Ya yabawa ‘yan takara, wakilai, jami’an jam’iyya, da hukumomin tsaro bisa tabbatar da gudanar da aikin cikin tsari da lumana, sannan ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da zama daya gabanin zaben gama gari a Jihar Kano.

Marigayi shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya mulki Najeriya daga 1993 zuwa 1998.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here