Abba kyari ya musanta zargin mallakar manyan kadarori 14 da aka bankado.

images 11 2
images 11 2

Fassarawa:Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Dakataccen Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari, ya musanta mallakar wasu kadarori guda 14, inda ya ce kadarorin da gwamnatin tarayya ta bankado ba nasa ba ne.

Tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan me tasarrafi da bayanan sirri, ya ce sabanin wasu makudan kudade da aka ce an gano a asusun ajiyarsa na banki, Abu na zahiri Naira miliyan 2 da dubu 800 ne kacal a asusunsa na UBA da kuma wasu Dubu 200 a cikin bankin sa na sterling.

Musantawar da Abba Kyari yayi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da wasu kafafen labarai suka fitar, cewa gwamnatin tarayya ta bankado wasu kadarori 14 da suka hada da kantuna, gidajen zama, filin wasan Polo, filaye da filayen noma mallakarsa.

Awata Sanarwa da lauyansa, Barr. Hamza Dan tani ya fitar ya yi ikirarin cewa, “dukkan zargin da hukumar NDLEA ta yi kan kudi da kadarori, Abba Kyari yace karya ce tsagwaron ta don kawai a yaudari jama’a su yi imani da cewa na Abba Kyari ne.”

Cikakkiyar Sanarwar ta ce, “‘yan kasuwa da ke da mallaki wadannan kadarorin kuma suka ba da takardunsu tuni sun shigar da hukumar NDLEA kara a babbar kotun tarayya dake Maiduguri.”

Cikakken bayanin sanarwar nacewa: “An ja hankalinmu kan wasu labaran karya da aka buga a wasu sassan kafafen labarai na ranar Litinin, 5 ga watan 2022 inda jaridun suka ce “Gwamnatin Tarayya ta bankado wasu kadarori 14 da suka hada da kantuna, gidajen zama, filin wasan Polo, filaye da filayen noma mallakar wata kasuwa Kuma ake alakanta su ga tsohon kwamanda kulada tasarrafi bayanan sirri Abba Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda.

“Muna so mu ja hankali don jama’a su san gaskiyar batu kan wannan lamarin.

“Hakazalika, NDLEA tana daukar nauyin wasu mutane don yada labaran karya, da zarge-zarge a Kotu ba tare da hujja ba.

“A ranar 29 ga watan Agusta 2022, babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja karkashin mai shari’a Inyang Eko ta yi watsi da karar da babban mai shari’a na tarayya ya shigar na mika DCP Abba Kyari ga Amurka.

“A ranar 30 ga watan Agusta, NDLEA ta sake shigar da kara tuhume-tuhume 24 kan Dcp Abba Kyari don kawai a batawa jama’a lokaci tare da bata masa suna duk da cewa maganar tana gaban babbar kotun tarayya da ke Maiduguri ba tare da wata shaida da ta alakanta Abba kyari da dukiyoyin ba.

Hukumar NDLEA batare hujjoji ba ta je ta yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba makarkashiya akan dukiya mallakin su, Sannan Hukumar ta fitar da rahotanni ga manema labarai wanda suka fara yadawa a watan Afrilun 2022.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here