Hukumomi a kasar Birtaniya ta damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, tare da matar sa kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.
Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo dan wani kasar kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya. Read
Wadan da ake zargi Beatrice Nwanneka Ekweremadu mai shekara 55, da kumaIke Ekweremadu, 60, zasu hallara a gaban kotu yau Alhamis.













































