Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne sun kai hari wani masallaci a ƙauyen Dadinkowa da ke Ƙaramar Hukumar Maiyama a Jihar Kebbi
Yayin harin sun kashe masu ibada shida tare da jikkata wasu uku, a wani hari da hukumomin tsaro suka bayyana a matsayin ramuwar gayya bayan yunkurin kwanton bauna da ya ci tura.
Maharan sun kutsa cikin masallacin ne a yammacin Laraba yayin da jama’a ke tsaka da gudanar da sallah, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kebbi, Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin ramuwar gayya ne da ake zargin wasu daga cikin ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai bayan sun kasa kai wa dakarun rundunar shiyya ta 8 Dmhari a wani kwanton bauna.
A cewarsa, lamarin ya samo asali ne tun ranar 24 ga Fabrairu lokacin da Babban Kwamandan Rundunar kuma Kwamandan shiyya ta 2 na Operation FANSAN YAMMA, Bemgha Koughna, ya fuskanci hari yayin da yake kan hanyarsa ta ziyartar dakarun da ke bakin aiki a jihar.
Ya ce ayarin motocin kwamandan ya fada cikin ruwan wutar ‘yan ta’addan a wani daji kusa da Tudun Mayama, inda dakarun suka mayar da martani da karfi tare da hallaka biyar daga cikin maharan.
Ya kara da cewa mutane biyar ne suka mutu nan take sakamakon harbin bindiga a harin masallacin, yayin da uku suka samu raunuka daban-daban aka kai su asibiti domin samun kulawa.
Sai dai, yayin gudanar da sallar jana’iza, an fito da gawawwaki shida domin jana’izar.













































