Yanzu-yanzu: ADC da NNPP sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026

Tinubu 1

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da New Nigeria Peoples Party (NNPP) a ranar Alhamis sun yi watsi da Dokar Zabe ta 2026 da Majalisar Tarayya ta amince da ita kuma Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba mata hannu.

Sun bayyana dokar a matsayin wadda ba ta inganta a dimokuradiyya ba, tare da zargin cewa an tsara ta ne domin karfafa tsarin jam’iyya daya a kasa.

A wani taron manema labarai, shugabannin jam’iyyun biyu sun sha alwashin amfani da duk hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada domin kalubalantar aiwatar da dokar.

Sun jaddada kudirinsu na kare dimokuradiyya da tabbatar da cewa kuri’un ‘yan Najeriya sun yi tasiri a zaben 2027.

Daga cikin manyan wadanda suka halarci taron akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi, tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, shugaban ADC na kasa David Mark, sakataren ADC na kasa Rauf Aregbesola, tsohon gwamnan Jihar Cross River Liyel Imoke, da shugaban NNPP na kasa Ajuji Ahmed.

Sauran sun hada da tsohuwar ‘yar majalisa Linda Ukeje, Dino Melaye, Bolaji Abdullahi, Buba Galadima, Lawal Batagarawa, Salihu Lukman da Yunusa Tanko.

Taron ya kuma nuna rabuwar kai a cikin ‘yan adawa, bayan wani bangare na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki ya fice daga wajen taron sakamakon rashin ba su damar karanta sanarwar da suka shirya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here