Sarkin Ilorin ya taya ‘yan asalin masarautar uku murnar samun matsayin SAN

Emir of Ilorin Ibrahim Sulu Gambari 750x430

Sarkin Ilorin kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya taya lauyoyi uku ‘yan asalin Masarautar Ilorin murna bisa daga darajar su zuwa matsayin Babban Lauyan Kasa (SAN).

Mai Martaba Sarkin ya bayyana cewa wannan karramawa mai girma shaida ce ta jajircewa, kwazo da sadaukarwar wadanda aka daukaka ga bangaren lauyanci.

Sakon taya murna na kunshe ne cikin sanarwar da Kakakin Sarkin, Dr. Abdulazeez Arowona ya fitar a ranar Lahadi.

SolaceBase ta ruwaito cewa Kwamitin Lauyoyi (LPPC) ya amince da daga darajar sabbin lauyoyi zuwa matsayin SAN kwanakin baya, matsayi mafi girman a bangaren aikin da ake bai wa lauyoyi a Najeriya saboda gagarumar gudunmawar da suka bayar a fannin shari’a da gudanar da adalci.

A cewar sanarwar, sabbin lauyoyin da aka tabbatar daga Masarautar Ilorin a cikin jerin na 2026 da LPPC ta fitar su ne Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar Kwara, Barr. Sulyman Ibrahim, Barr. Mas’ud Alabelewe da Barr. Mohammed Adelodun.

Sarkin Ilorin ya ce wannan daga daraja ta nuna kwarewa da jajircewar wadanda aka yiwa ga aikin lauyanci.

Ya ce “Matsayin SAN shi ne mafi girman alamar kwarewa da ake bai wa lauyoyin da suka nuna bajinta a kotuna.”

Sarkin ya bukaci sabbin Babban Lauyoyin da su rika kiyaye ka’idoji, mutunci da darajar sana’ar lauya, sannan su zama abin koyi ga matasan lauyoyi.

“A madadin Masarautar Ilorin da al’ummar Jihar Kwara baki daya muna mika murna ga wadannan fitattun lauyoyi bisa wannan daukaka da suka cancanta. Allah Madaukaki ya ba su karin hikima domin su ci gaba da bayar da gudunmawa wajen tabbatar da adalci da bunkasa kasa,” in ji Mai Martaba.

Sarkin ya kuma yaba wa Kwamitin LPPC saboda yadda ya karrama hazaka da ganin ‘ya’yan Masarautar Ilorin sun cancanci wannan karramawa mai girma.

Sannan ya yi addu’ar Allah ya yi wa sabbin Babban Lauyoyin jagora, kariya da nasara a sabon matsayinsu domin amfanin kasa da al’umma baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here