Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fitar da dala miliyan 6 daga asusun bayar da agajin jin kai na Najeriya don taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.
Mohammed Fall, mai kula da ayyukan jin kai a Najeriya ne ya bayyana hakan bayan rugujewar madatsar ruwa ta Alau a ranar 10 ga watan Satumba, wanda ya raba dubban mazauna kusa da Maiduguri, babban birnin jihar.
A yayin ganawa da manema labarai, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana irin kokarin da hukumomin MDD, kungiyoyi masu zaman kansu, da kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya suka yi, wadanda suka ziyarci Maiduguri kwanan nan domin duba halin da ake ciki.
Yawancin wadanda abin ya shafa sun riga sun yi gudun hijira sau da yawa saboda rikice-rikice da rashin tsaro a yankin.
Dujarric ya lura cewa, Majalisar Dinkin Duniya da abokan huldarta na samar da abinci mai zafi, da isar da abinci zuwa yankunan da ke da wuyar isa, da ruwa mai tsafta, da kuma ayyukan tsafta don hana barkewar cututtuka. Suna kuma rarraba kayan tsafta da mutunci ga mata da ‘yan mata, tare da samar da lafiya da matsuguni na gaggawa.
A halin da ake ciki, Emmanuel Bigenimana, shugaban ofishin hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) a Maiduguri, ya bayyana damuwarsa bayan gudanar da bincike cikin gaggawa ta sararin samaniya na barnar da aka yi.
Ya bayyana irin barnar da aka yi, inda gidaje, ababen more rayuwa, tituna, da makarantu suka mamaye da ruwa.
Kimanin mutane 200,000 – 300,000 ne cunkoson jama’a a sansanonin ‘yan gudun hijirar (IDP) da tituna, da yawa daga cikinsu ba su da matsuguni da kayan masarufi.
Bigenimana ya ce WFP ta bude wuraren dafa abinci na miya a sansanonin ‘yan gudun hijira uku, da nufin samar da abinci mai gina jiki ga mutane 50,000 daga cikin wadanda abin ya fi shafa.
Koyaya, ana buƙatar ƙarin albarkatu don ci gaba da ayyukan agajin da ke gudana. Ambaliyar ruwan wadda ta shafi mutane sama da 800,000 a fadin Najeriya, ta kara dagula matsalar karancin abinci da tuni aka fuskanta.