Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa an samu raguwar aikata laifuka sosai a fadin jihar a cikin watanni uku na farkon shekarar 2026, inda ta danganta hakan da sabbin dabarun aikin ‘yan sanda, amfani da bayanan sirri da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a hedikwatar rundunar da ke Bompai a Kano, inda ya yi bayani kan halin tsaro a jihar.
Bakori ya ce sake fasalin rundunar da aka yi ya inganta yadda ake gudanar da ayyuka tare da ƙara saurin amsa barazanar tsaro, yana mai cewa sauye-sauyen da ake yi suna fara haifar da sakamako mai kyau wajen tabbatar da doka da oda.
Ya ƙara da cewa rundunar na da ƙudurin ci gaba da wannan nasara domin tabbatar da cewa Kano ta ci gaba da kasancewa wuri mai aminci ga mazauna da kuma masu kasuwanci.
Da yake bayani kan tsare-tsaren rundunar na shekarar 2026, kwamishinan ya ce dabaru irin su aikin ‘yan sanda na al’umma, amfani da bayanan sirri, ƙarfafa ƙwarewar jami’ai da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomi sun taimaka wajen inganta tsarin tsaro a jihar.
Musamman ya ambaci nasarar aikin “Kukan Kura”, wanda ya ce ya taimaka matuƙa wajen rage ayyukan daba da ake kira fadan daba a cikin gari.
Ya kuma bayyana cewa an kare jihar daga shigowar ‘yan bindiga ta hanyar haɗin gwiwa da gwamnatin jihar Kano da sauran hukumomin tsaro, yayin da aka warware rikice-rikicen manoma da makiyaya ta hanyar tattaunawa da hulɗa da al’umma.
Haka kuma, ya ce rundunar ta yi amfani da bayanai daga jama’a domin gano masu safarar miyagun ƙwayoyi, inda aka samu sama da sunaye 2,000 daga jama’a, kuma wasu daga cikinsu sun maimaitu, abin da ke nuna sahihancin bayanan.
Ya ce ana ci gaba da tantance waɗannan mutane domin ɗaukar matakan da suka dace, yana mai jaddada muhimmancin amfani da fasaha da kuma haɗin kan al’umma wajen yaƙi da laifuka.
Bakori ya ƙara da cewa an kama mutane da dama da ake zargi da aikata laifuka kamar fashi da makami, satar mutane, laifukan internet da safarar miyagun ƙwayoyi, tare da ƙwato kayayyakin da aka sace a lokuta daban-daban.
Duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale, ya tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin magance matsalolin tsaro.
Ya kuma gode wa Babban Sufeton ‘yan sanda da kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayan da suke bai wa rundunar, tare da yabawa al’ummar jihar kan haɗin kan da suke bayarwa.
Ya buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai a kan lokaci, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.










































