
Majalisar dokokin jihar Kano ta samu takarda daga gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa neman majalisar ta duba tare da amincewa da bukatar kafa cibiyar yaki da cututtuka ta jihar Kano.
Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa an karanta wasikar da aka aika wa shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore a zauren majalisar a ranar Litinin da ta gabata ta hannun kakakin majalisar.
Wata sanarwa da Uba Abdullahi, Babban Sakataren Yada Labarai ya raba wa Majalisar, ta ce wani bangare na cikin wasikar ya bayyana cewa, idan aka kafa cibiyar za ta gaggauta magance bullar cutar a jihar.
Karanta wannan: Sojin Ghana ya mutu a aikin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
Hakazalika majalisar ta samu rahoto daga zaunannen kwamitin kula da harkokin zabe na majalisar dangane da tantance wanda aka zaba Farfesa Sani Lawan Malumfashi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano.
Rahoton wanda shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Hussaini Dala ya karanta, ya ce kwamitin ya gano wanda aka zaba ya cancanta kuma ya cancanci nadin.
Karanta wannan: Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota a Jihar Niger
A cewar sanarwar, wani bangare na shawarwarin kwamitin ya bayyana cewa Farfesa Sani Lawan Malumfashi bisa la’akari da tarihinsa kuma bisa ga dokar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano na 2001 ya cancanci wannan nadin.
Majalisar ta dage zamanta zuwa gobe Talata, a wani kudiri da shugaban masu rinjaye, Lawan Hussaini Dala ya gabatar, kuma shugaban marasa rinjaye Labaran Abdul Madari ne ya goyi bayansa.












































