Amarya da kawayenta sun mutu a hatsarin mota a Jihar Niger

hadarin, mutu, niger
Wata sabuwar amarya da kawayenta biyar sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kusa da Lukoro da ke garin Edati a jihar...

Wata sabuwar amarya da kawayenta biyar sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kusa da Lukoro da ke garin Edati a jihar Niger a ranar Juma’ar da ta gabata.

Jumullar mutane 13 ne suka rasa rayukansu a hatsarin motar da suka hada da sirikin amaryar da wasu karin mutane 6 kamar yadda FRSC, ta bayyana, tana mai danganta hatsarin da gudun wuce sa’a.

Bayanai na cewa, motocin da suka yi taho mu gaman sun hada da kirar Toyota Corolla wadda ta taso daga Mokwa zuwa Bidda da kuma motar bas ta ‘yan kasuwa kirar Nisan da ke kan hanyarta ta zuwa Minna, babban birnin jihar Niger zuwa Ogbomoso da ke jihar Oyo.

Karanta wannan: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da ango da amarya a Jihar Zamfara

Babban Kwamandan Hukumar FRSC, reshen jihar Niger, Tsukwan Kumar, ya ce an samu asarar rayukan mata takwas da kuma maza hudu, sai kuma wani karamin yaro guda.

Tuni aka mika gawarwakin mutane 9 ga iyalansu, yayin da sauran mamatan aka garzaya da su dakin ajiyar gawarwaki da ke babban asibitin koyarwa na Kutigi kamar yadda Mista Kumar ya bayyana.

Ana yawan samun asarar rayukan al’ummar Najeriya a hadduran motoci da masana ke dangantawa da musabbabai daban-daban da suka hada da tsananin gudu da lalacewar hanya da tukin ganganci da rashin hakuri da dai sauransu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here