Wani babban dan jam’iyyar ADC Kenneth Okonkwo, ya ce goyon bayan Peter Obi a zaben shugaban kasa na 2027 zai karfafa damar Shugaba Bola Tinubu na sake cin zabe ne kawai.
Okonkwo ya bayyana hakan ne a cikin tattaunawa da Symfoni TV, inda ya jaddada bukatar jam’iyyun adawa su hade a jam’iyya daya idan suna son kada shugaba mai ci a babban zaben da ke tafe.
A cewarsa, raba jam’iyyun adawa zai saukaka wa Tinubu wajen samun wa’adi na biyu.
“Dalilin da yasa na fadi haka shi ne, ko kai ka na yiwa Tinubu aiki kai tsaye, wato kai dan APC ne, ko kuma ka na yi masa aiki ta wata hanyar. Saboda idan ka raba kuri’un hadin gwiwa da na adawa, har yanzu kana sake baiwa Tinubu dama ne don sake yin nasara,” in ji Okonkwo.
Tsohon kakakin jam’iyyar Labour Party ya kuma soki rahoton cewa Obi ya fice daga tattaunawar hafin gwiwa a cikin ADC, inda ya zargi tsohon dan takarar shugaban kasar da cewa ba ya son shiga zaben fidda gwani.
“Ba za ka iya tsayawa takara a zaben fidda gwani ba, sannan kana son zama dan siyasa, kana son zama shugaban kasa mai cike dakalubale, sannan ka na gudu daga kalubale,” in ji shi.
Okonkwo ya kara da cewa Sanata Victor Umeh ya taba bayyana ra’ayin cewa hanya mafi kyau ga Kudu maso Gabas ta samu shugaban Najeriya ita ce ta hada gwiwa da shugabannin Arewa.
“Lokacin da muka shiga ADC duka, Victor Umeh ya bayyana a sarari kuma ya fada mini da kansa cewa hanya daya tilo da ’yan Igbo ke da ita, ita ce su yi kawance da Arewa, kuma dan’uwanmu Peter Obi ya zama mataimakin shugaban ƙasa,” in ji Okonkwo












































