Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta musanta rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su a garueuwan Ahoro, Esiele da Yawota da ke Karamar Hukumar Oriire sun shaki iskar ‘yanci.
Rundunar ta ce rahotannin ba gaskiya ba ne, inda ta bayyana su a matsayin na karya da za su iya kawo cikas ga kokarin ceton da ake yi.
A cikin sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, DSP Olayinka Ayanlade, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce hukumomin tsaro ba su samu irin wannan nasarar ba da ake yadawa, ta kuma bukaci al’umma su yi watsi da rahotannin da ke yawo.
“Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo tana musanta gaba ɗaya saƙonnin da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke zargin cewa ’yan makaranta da malamai da aka sace daga al’ummomin Ahoro, Esiele da Yawota na Karamar Hukumar Oriire a Jihar Oyo, masu garkuwa da su sun sake su.
’Yan sandan sun tabbatar wa iyalai da al-ummar jihar cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri don ceto, inda jami’an tsaro ke daukar duka matakai don tabbatar da dawowar wadanda aka sace cikin aminci.












































