An yankewa Adawale da wasu mutane 5 hukuncin rataya a jihar Ondo

Adawale, rataya, hukunci, rataya, jihar, Ondo
Babbar kotun jihar Ondo ta samu Adawale da abokansa da laifin kai hari tare da yin fashi a wasu bankunan kasuwanci a Akure, babban birnin jihar da kuma garin...

Babbar kotun jihar Ondo ta samu Adawale da abokansa da laifin kai hari tare da yin fashi a wasu bankunan kasuwanci a Akure, babban birnin jihar da kuma garin Idanre.

Sun yi fashin ne shekaru 13 da suka gabata a reshen bankin Diamond Access da ke Akure da kuma reshen First Bank da ke Idanre, hedikwatar Karamar Hukumar Idanre.

Karin labari: Ghana na zargin ‘yan siyasa da sarakuna kan ayyukan masu hakar ma’adanai

Mai shari’a Yemi Fasanmi wanda ya jagoranci shari’ar ya yanke musu hukuncin ne bayan sun amsa cewa sun aikata laifin da ake tuhumar su.

A ranar 14 ga watan Yulin 2022 aka fara gurfanar da su kan zargin hada baki, fashi da makami, da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Bayan gurfanar da su a gaban kotu, alkali ya bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Olokuta da ke jihar.

Karin labari: Kwastam za ta rabawa jama’a kayan abincin da ta kwace

A yayin shari’ar, lauya mai gabadatar da kara Salami, ya gabatar da shaidun da ke nuna cewa wadanda aka yankewa hukuncin, sun yi amfani da nakiyoyi da kuma bindigogi kirar AK-47 wajen yin fashin a rasssan bankunan, lamarin da ya girgiza al’ummar Akure da Idanre.

Bayan kowannensu ya amsa irin rawar da ya taka a fashin bankunan, Mai Shari’a Fasanmi, ya yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan kowanne daga cikin laifukan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here