Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya miƙa ta’aziyyar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga gwamnati da al’ummar jihar Kwara kan kisan gillar da aka yi a Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai jihar a madadin shugaban ƙasa, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin tausayi da girgiza zuciya, yana mai cewa waɗanda suka rasu mutanen kirki ne da ke gudanar da halaltattun sana’o’i cikin lumana.
A ziyarar, Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar gwamnan jihar Borno Umara Zulum, darakta janar na hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA Zubaida Umar, sanata Ali Ndume, da daraktar gudanarwa ta kamfanin wutar lantarki na yankin Neja Delta NDPHC Jennifer Adighije, tare da wasu manyan jami’ai da tsofaffin ‘yan majalisa.
Da isarsu filin jirgin saman Tunde Idiagbon na duniya da ke Ilorin, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya tarbe su tare da mambobin majalisar zartarwa ta jihar da sauran manyan jami’an gwamnati.
Shettima ya bayyana cewa al’ummomin da abin ya shafa sun dade suna rayuwa cikin zaman lafiya da koyarwar addinin Musulunci mai cike da haƙuri, yana mai cewa tashin hankalin ya sabawa tarihinsu, al’adunsu da koyarwar addininsu, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta tura rundunar sojoji domin dawo da zaman lafiya da tsaro.
Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasa ya umarci hukumar NEMA ta haɗa kai da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Kwara domin tattara kayan agaji da bayar da tallafin jin ƙai ga waɗanda abin ya shafa, tare da yin addu’ar rahama ga waɗanda suka rasu da kuma haƙurin jure rashin ga iyalansu.
A nasa martanin, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya gode wa shugaban ƙasa da Mataimakin shugaban ƙasa, yana mai bayyana matakin gwamnatin tarayya a matsayin mai sauri da kwantar da hankali.
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun bazu a yankin yayin da jami’an NEMA ke ci gaba da tantance buƙatun jin ƙai.
NAN













































