Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta ce za ta ɗauki matakin hukunta ɗaliban da ba sa zuwa makaranta kasancewar gwamnati ta samar da tsarin ilimi dole kuma kyauta.
Yayin da a gefe guda kuma iyaye suka fara tofa albarkacin bakinsu game da yunƙurin da hukummomi ke yi na hukunta iyaye da yaran da basa zuwa makaranta kuma suke gararamba a kwararo a jihar Kano.
Sai dai iyaye da dama na ganin ya kamata gwamnati ta fara kyautata ilimi a gani a kasa kafin a dauki irin wannan mataki.
Karanta wannan: Gwamnatin Tarayya ta yi barazana da takunkumi kan ma’aikatan Gwamnati
Haruna Doguwa, kwamishinan ilimi na jihar Kano a wani sakon murya da ya aikewa BBC a ranar Talata, ya ce ɗaya daga cikin matakin da za’a ɗauka wajen hukunta yaran da ba sa zuwa makaranta shi ne bayar da kashedi na farko idan suka sake sai a bayar da kashedi na biyu, bayan wannan kuma suka sake aikata laifin sai dai kawai a dakatar da su.
Wannan dai wani yunkuri ne da gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen taimakawa yaran da su ke yawace-yawace a lungu da sako da wasu tituna na jihar.