Gwamnatin Jihar Legas ta bada umarnin Rufe Makarantun Chrisland dake Fadin Jihar

Chrisland Schools 678x381 1
Chrisland Schools 678x381 1

Gwamnatin Jihar Legas ta bada umarnin da a gaggauta rufe Makarantar Chrisland dake Jihar, har sai an kammala binciken Faifan Bidiyon nan na zargin Fyade ga dalibar Makarantar Yar shekaru 10 a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kwamishinan Ma’aikatar ilimi na jihar Folashade Adefisayo, shi ne ya bada umarnin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, bayan da Faifan Bidiyon fyaden ya ci gaba da zagayawa.

Haka kuma, tun a ranar 14 ga watan Afrilu hukumar makarantar ta dakatar da Yarinyar Yar shekaru 10 dake cikin Faifen Bidiyon daga zuwa Makaranta.

A cikin wasikar dakatarwar, hukumar makarantar ta zargi dalibar da shiga cikin wani wasa ‘Gaskiya ko Dare’ da ya kai ga aikata mata “fyaden”.

Sun je birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa ne domin halartar gasar wasannin Makarantu ta Duniya da aka gudanar tsakanin 10 zuwa 13 ga Maris.

Wasikar, mai kwanan wata 14 ga Afrilun shekarar 2022, mai dauke da sa hannun Shugaban Makarantar, G. I. Azike, mai taken, “Dakatar da…(an boye sunayen).”

Wasikar daga gwamnatin jihar Legas ta kara da cewa: “An jawo hankalin gwamnatin jihar ne kan zargin cin zarafin daliban makarantar Chrisland, wanda ya faru a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

“Sakamakon zarge-zargen, mun himmatu wajen tabbatar da an samar da isassun tallafin jinya.

“Bukatarmu shi ne kara tabbatar wa al’umma kudirin Gwamnatin Jiha na tabbatar da tsaro da kare hakkin yara, musamman wajen tabbatar da cewa duk cibiyoyin da suka shafi kananan yara a jihar, su tsara tare da aiwatar da tsare-tsaren yadda suka dace da Dokar bangaren Zartarwa (NO.EO). /AA08, na dokar Kare hakkin Yara ta Jihar Legas da aka yiwa gyara a shekarar 2016.

“Muna amfani da wannan kafar don tunatar da jama’a cewa duk mutumin da ya aikata wani abu da ya shafi cin zarafin yara, to ya sani ya aikata babban laifi kuma zai fuskanci hukuncin daurin shekaru goma sha hudu (14).

“A halin yanzu, an rufe dukkan makarantun Chrisland da ke jihar Legas, har sai yadda bincike ya yi.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here