Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge
Malaman da ke karkashin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Wudil a Kano sun fara yajin aikin gargadi na makonni biyu.
Malaman sun ce yajin aikin ya zama tilas ne a kan yadda gwamnatin jihar ke nuna halin ko in kula ga bukatunsu.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Laraba ne mambobin kungiyar ASUU na jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano suka ayyana yajin aikin gargadi na tsawon mako biyu.
Karin labari: Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar kungiyar kwadago
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ASUU reshen kuma mukaddashin sakataren kungiyar, Dakta Aliyu Yusuf Ahmad da Dokta Ya’u Sabo Ajingi suka fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce a kan haka ne, kungiyar ASUU reshen KUST, Wudil da ta taso daga taron CONGRESS na musamman da aka yi a ranar Laraba 29 ga watan Mayu, 2024 ta yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu nan take.
Karin labari: Tinubu ya saukakawa matafiya a tsarin sufurin jiragen kasa na Abuja zuwa Disamba
SolaceBase ta rawaito cewa, bukatun kungiyar sun hada da rashin mayar da hukumar gudanarwar jami’o’i, da rashin biyan wasu hakkokinsu da kuma rashin kudaden da jami’ar ke yi da kuma sauransu.
Sanarwar ta ce domin kauce wa ci gaba da tabarbarewar lamarin, reshen na amfani da wannan kafar wajen yin kira ga al’ummar jihar Kano da Najeriya da su yi nasara a kan gwamnati ta sa ido kan batutuwan da ke sama.