![Mafi Karancin Albashi: Gwamnatin tarayya ta sake gayyatar... NLC, gwamnatin, tarayya, kungiyar, kwadago, gayyatar](https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2024/05/NLC-z-696x399.jpeg)
Daga: Sununsi A. Dantalata Fagge
Gwamnatin tarayya ta sake mika goron gayyata ga kungiyar kwadago domin ci gaba da tattaunawa kan mafi karancin albashi, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.
“Shugaban kwamitin ya aike da wasika zuwa ga kungiyar kwadago kuma shugaban NSIWC ya sanya wa hannu. An shirya taron ne a ranar Juma’a.
“Tabbas, Labour za ta halarta. Idan suka gabatar da mafi kyawun tayi ranar Juma’a za mu karba,” wata majiya ta shaida wa jaridar.
Karin labari: Daraktoci 40 sun fadi jarrabawar cancantar zama sakatarori
SolaceBase ta rawaito cewa kwamitin mafi karancin albashi ya dage zaman a ranar Talata bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago ta wargaje, yayin da ma’aikata suka ki amincewa da sabon kudirin Gwamnatin Tarayya na Naira Dubu 60,000, sama da Naira Dubu 57,000 da ta gabatar a baya.
Shugabannin Kwadago sun ba da shawarar Naira 494,000 tare da bai wa kwamitin har zuwa karshen wata da ya kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi na kasa.
Wa’adin zai kare a daren Juma’a.
Karin labari: Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin maido da tsohuwar waka a matsayin doka
Sai dai Karamar Ministar Kwadago da Aiki, Nkeiruka Onyejeocha, a ranar Larabar da ta gabata, ta yi kira ga kungiyoyin kwadagon da su kasance masu la’akari da kishin kasa a kan bukatunsu a tattaunawar da ake yi na neman sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.
Ministan ya ce a ko da yaushe Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin tabbatar da daidaiton albashin ma’aikatan Najeriya.