Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da bada hutun Babbar Sallah ga makarantu

Abba Kabir Yusuf 750x430

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da bada hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

Sanarwar na cikin wata takarda da Daraktan Wayar da kai na Ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, daliban makarantun kwana za su fara hutunsu daga ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, za kuma su koma makaranta a Lahadi, 31 ga Mayun 2026.

Ta kuma kara da cewa makarantun jeka ka dawo za su fara hutunsu daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, yayin da karatu zai ci gaba daga ranar Litinin, 1 ga Yunin 2026.

Ma’aikatar ta kuma shawarci iyaye da masu kula da daliban dake makarantun kwana da su dauko ‘ya’yansu a ranar da aka ayyana za a rufe makaranta, tare da tabbatar da dawowarsu kan lokaci yayin da za a bude makaranta.

“Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da hutun Babbar Sallar ga dukkan makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar,” in ji sanarwar.

Kwamishinan Ilimi, Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi wa dalibai, malamai, iyaye da dukkan al’ummar ilimi fatan yin bikin Babbar Sallah cikin lumana da farin ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here