‘Yan sanda sun fara bincike kan mutuwar wani mutum mai shekaru 60 a otal a Jigawa

Police badge

Rudunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce ta fara bincike kan yanayin mutuwar wani mutum da ba a bayyana sunansa ba mai shekaru 60 da ya rasu ba zato ba tsammani a dakin otal a Dutse, babban birnin jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP Lawan Shiisu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Dutse.

Shiisu ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, bayan marigayin ya shiga otal din tare da wata yarinya mai shekaru 20 da aka ki bayyana sunanta, sannan ba dadewa ba samu matsalar lafiya ta gaggawa bayan ya nemi abinci.

Ya bayyana cewa bayan samun rahoton gaggawa, ‘yan sandan da ke Yalwawa sun je wurin da lamarin ya faru nan take sannan suka gaggauta kai marigayin zuwa Babban Asibitin Dutse, inda ma’aikatan lafiya suka bincike shi suka tabbatar da rasuwarsa.

“Bayan haka, jami’an binciken asiri na ‘yan sanda sun killace gurin da lamarin ya faru, kuma sun gudanar da binciken farko inda aka gano wasu kayan abinci, aubuwan sha, abun da ake zargi da zama maganin kara kuzarin jima’i sauran kayayyakin amfanin kai domin gudanar da bincike nag aba a matsayin wani bangare na binciken da ake tsaka da yi.

“Dukkan matakan da suka dace an bi domin kiyaye muhimman hujjoji da saukaka cikakken bincike.

“Bayan tabbatar da rasuwarsa da likitoci suka yi, an mika gawar marigayin ga iyalansa domin su yi jana’izar sa bisa bukatarsu,” in ji shi.

Mai magana da yawun ya kara da cewa yarinyar mai shekaru 20 da ke wurin a lokacin lamarin ta ba ‘yan sanda hadin kai wajen ba da bayanai masu amfani domin taimakawa wajen gano yadda lamarin ya faru.

Shiisu ya tabbatar wa jama’a cewa za a gudanar da binciken cikin tsari da adalci.

Ya bukaci mazauna jihar da su guji yin hasashe ko yada bayanan da ba a tabbatar ba da za su iya haifar da firgici ko cutar da binciken.
“Za mu fitar da karin bayani yayin da binciken ke ci gaba,” in ji Shiisu. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here