DA ƊUMI-ƊUMI: Kotu Ta Dakatar da Gwamnatin Tarayya daga Sake Gurfanar Tsohon Gwamnan Abia Urzo Kalu

Orji Uzor Kalu5
Orji Uzor Kalu5

Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta hana Gwamnatin Tarayya sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu, bisa zargin karkatar da Naira Biliyan 7.1 da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, ta fi shigar a kansa.

Kotun a ranar Laraba, karkashin Mai Shari’a Inyang Ekwo ta ce Kotun Koli ba ta yanke hukunci a ranar 8 ga Mayu, 2020 ba, na ba da umarnin a sake shari’ar Kalu ko kamfaninsa, Slok Nigeria Limited.

Mai shari’a Ekwo ya ce Kotun Koli ta ba da umarnin a sake gurfanar da tsohon Daraktan Kudi a Jihar Abia, Jones Udeogu, wanda shi ne mai daukaka kara gabanta.

A sakamakon haka, ya goyi bayan karar da Kalu ya shigar don kalubalantar sahihancin shari’ar da hukumar EFCC ke shirin yi na sake gurfanar da shi.

Kalu a cikin korafe-korafen da ya shigar ta hannun lauyoyin sa Chief Awa Kalu, SAN, ya bayar da hujjar cewa barin EFCC ta sake gurfanar da shi a kan tuhumar da kuma irin hujjojin da aka riga aka yanke masa hukunci a ranar 5 ga Disamba, 2019, zai wuce gona da iri. Kuma tamkar wahalarwa ce”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here