Babu Amfanin Cece-Kuce Saboda An Baiwa Sarkin Kano Kyautar Mota-kungiyar DAH

Rolls Royce
Rolls Royce

Wata kungiya mai zaman kanta ta “Defenders of Arewa Heritage (DAH)”, tace bai kamata a cigaba da cece-kuce da suka akan kyautar mota kirar “Rolls Royce” da aka baiwa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Kungiyar tana tsokaci ne kan labarin da wani attajirin dan kasuwa kuma shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, da ya bai wa sarkin Kano kyautar Rolls Royce Phantom.

Sanarwar da daraktan zartarwar kungiyar Idrissa Mala da jami’in sadarwa Hakeem Raji suka sanya wa hannu a ranar Talata, ta ce “babu wani laifi ga kyautar mota da attajirin dan kasuwan ya bayar.”

Ta kuma ce “yadda wasu kafafen yada labarai suka yi ta yayata labarin ne har ya sa ake neman siyasantar da kyautar.”
Kungiyar tace ana baiwa sarakunan gargajiya a fadin kasar nan kyaututtukan alfarma da motoci daga abokansu da ya yan uwa. Bambancin wannan kyautar ta BUA kawai itace an yada ta a kafafen yada labarai.

Bayanin ya kara da cewa ba a kano kadai bane ake baiwa sarakuna kyautar moroci na alfarma. “Kamar a jihar Borno, babban dan kasuwa Muhamamd Indimi da marigayi Ahmed Mai Deribe, da Bukar Mandara sun taba bayar da kyautar motoci ga shehun Borno a lokaci daya amma kuma ba a yayata labarin ba” a cewar kungiyar.

Kungiyar ta ce an taba baiwa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II motoci kirar Rolls Royce Phantom guda biyu yayin da yake kan karagar mulki.

“Wadanda suka bada kyautar basu sanar a kafofin watsa labarai ba. ‘Yan Najeriya ba su taba sani ba cewa abokan Sarki Sanusi biyu ne suka bashi kyautar “Rolls Royces”: Mista Kola Kareem da Hajiya Bola Shagaya.

“Saidai shi sarkin da kansa ya wallafa sunayen mutanen da suka bashi kyautar a lokacin da aka zarge shi da amfani da kudin masarautar wajen siyan motocin” a cewar bayanin.

Kuma tsohon sarkin ya kare kyautar da aka bashi da cewa ba wani sabon abu bane. “Motocin kirar Limozin na marigayi Sarki Ado Bayero, Aminu Dantata da Fernandez, Isiaka Rabiu, Sani Abacha da Ahmed Mu’azu ne suka bayar, kuma kowa yana da abokai da masu fatan alkhairi.

Kungiyar tace hakan yasa “Muke ganin yayata batun kyautar motar da aka bayar bashida wani amfani.”

Tace wallafa labarin an bada kyautar miliyan 100 baya ga motar shi kansa bai kamata ba. Muna tunanin kawai ana hakan ne domin wata manufa kokuma bayyana sarkin ga ‘yan bindiga.

Kungiyar ta ce yada labarin kyautar “baya cikin dabi’u na gari da al’adun ‘yan arewa da kuma koyarwar addinin Musulunci.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here