Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana dan takarar Jam’iyyar APC, Gwamna Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar ranar Asabar.
An sake zabar gwamnan ne bayan ya samu kuri’u 319,224 fiye da abokan hamayyarsa na kusa daga jam’iyyar adawa ta PDP, Olumayokun Oluyede da na ADC Dare Bejide, a kananan hukumomi 16 na jihar.
Jami’ar da ta ayyana sakamako ta kuma tabbatar, Farfesa Adenike Oladiji, wadda ita ce Shugabar Jami’ar Kimiya ta Tarayya da ke Akure, ta sanar da sakamakon da safiyar ranar Lahadi a hedkwatar hukumar da ke kan titin Iyin a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
Oladiji ta ce, “Saboda haka, ni, Adenike, ni ce jami’ar da ke ayyana sakamako na zaben gwamnan Ekiti na 2026… Oyebanji Abiodun Abayomi, ganin ya cika sharuddan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma an tabbatar da zabensa.”
Yayin da APC ta samu kuri’u 319,224, dan takarar PDP ya samu kuri’u 40,533, sai kuma dan takar lar ADC kuma ya samu kuri’u 12,872.
Akwai masu rajista 988,251, kuma aka tantance masu jefa kuri’a 384,940.
Daga cikin kuri’u 382,109 da aka jefa, jimillar kuri’u masu inganci a zaben su ne 375,777.
A cewar sakamakon, dan takarar PDP, wanda dan asalin Ikere Ekiti ne, ya sha kaye a karamar hukumar Ikere inda ya fito.
Yayin da APC da dan takararta Oyebanji suka samu kuri’u 8,742, PDP, wadda ta zo ta biyu a karamar hukumar, ta samu kuri’u 2,051.










































