Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a ranar Asabar ta fara nuna bayanai na musamman na ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka gabatar don zaben gama gari na 2027.
Ta ce wannan na cikin tanadin Dokar Zabe ta 2026 ne.
Matakin wanda ya yi daidai da sabon Jadawalin Lokaci da Ayyuka na zaben 2027, wani bangare ne na takardun neman takara da ‘yan takarar da ke son yin takarar zaben Shugaban Kasa na 16 ga Janairu, 2027 suka mika.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, INEC ta ce an gudanar da wannan aiki a Babban Ofishinta na Kasa da ke Abuja, da kuma a dukkan ofisoshin Hukuma 6 na Birnin Tarayya lokaci guda. Manufar shi ne tabbatar da gaskiya da baiwa wa jama’a damar bincikar takardun cancanta da sauran bayanan da ‘yan takarar da ke neman mukamai suka mika.
Babbar Sakatariyar Gudanarwa, Bimbo Oladunjoye, wadda ta wakilci Kwamishinan Zabe na Birnin Tarayya (REC) a lokacin aikin, ta ce wallafa bayanan ‘yan takara wani sharadi ne na doka bisa Sashi na 29(3) na Dokar Zabe ta 2026. Wannan sashi na bukatar Hukumar ta nuna bayanan sirri, da sauran takardun da suka dace na ‘yan takara a matakan da suke son yin takara.
Oladunjoye ta bayyana cewa bayyana bayanan ya shafi ‘yan takarar Shugaban Kasa da ‘yan Majalisar Kasa da ke takara a Babban Birnin Tarayya, inda ta kara da cewa ana gudanar da aikin lokaci guda a dukkan ofisoshin hukumar a hankuna 6 domin saukaka wa jama’a samun damar shiga.
Ta ce nuna bayanan ‘yan takara wani muhimmin bangare ne na tsarin zabe, domin yana karfafa gaskiya, amana da amincewar jama’a ga yadda ake gudanar da zabe. Ta bukaci ‘yan kasa, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin jama’a, kafofin yada labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan dama wajen duba bayanan da aka nuna sosai.
A cewarta, Hukumar ta himmatu wajen bin doka da aiwatar da Jadawalin Lokaci da Ayyuka na Zaben 2027.













































