Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi nade-nadensa na farko a matsayin Shugaban Kasa.
Tinubu dai ya nada Ambasada Kunle Adeleke mai tsare-tsaren Shugaban Kasa.
Kazalika, ya nada tsohon Kwamishinan Yada Labaran Jihar Legas, Dele Alake a matsayin Kakakinsa.
Bugu da kari, Shugaban ya kuma nada Olusegun Dada a matsayin Hadiminsa na bangaren kafafen sada zumunta na zamani.













































