Mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a hannun masu garkuwa ya kamata ya damu kowane dan Najeriya. Sama da asarar babban jami’in soja mai daraja, lamarin ya bayyana zahirin gaskiyar da zai yi wahala a kauda kai, rashin tsaro a Najeriya ya kai matakin da babu wanda zai iya cewa ba zai same shi ba.
Shekaru da dama rashin tsaro ya kasance daya daga cikin manyan kalubalen da kasar ke fuskanta. Ko da yake rikicin ya kara bayyana a shekarun baya-bayan nan na da asalin a baya.
Najeriya ta dade tana fama da rikice-rikicen kabilanci, fashi da makami, ta’addanci, rikicin addini da kabila, da raunin gwamnati a wasu sassan kasar.
Boko Haram ta fara ne a farkon shekarun 2000 kafin ta zama cikakkiyar kungiyar tawaye zuwa shekara ta 2009. Tun daga lokacin, gwamnatoci daban-daban sun gaji kalubalen kuma sun yi alkawarin samar da mafita, amma matsalar ta ci gaba da wanzuwa maimakon ta kare.
Yayin da wata barazana ke raunana, wata kuma tana bayyana, yayin da hankalin kasa ya kasance kan ‘yan tawaye a Arewa maso Gabas, wasu kungiyoyin masu aikata laifuka suka sami damar a wasu wurare.
A manyan sassan Arewa maso Yamma, satar shanu, hako ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yawaitar kananan makamai, da fafatawa kan karancin albarkatu sun haifar da matsalar ‘yan bindiga.
Abin da da farko ake ganin kawai laifuka ne na mutane tsirari, ya rikide zuwa kungoyoyi manya da ke kai hari kan al’ummomi, yin garkuwa da mutane, sace shanu, da fuskantar jami’an tsaro.
A halin da ake ciki, rikice-rikicen kabilu da na addini sun ci gaba a sassan Tsakiyar Najeriya, yayin da sace mutane domin neman kudin fansa ya bazu a manyan hanyoyi da al’ummomi a sassa daban-daban na kasar.
Yau, rashin tsaro ya wuce iya wani yanki, ta zama matsalar kasa baki daya da ke shafar al’ummomin birane da na karkara.
Mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe a hannun masu garkuwa tana da mahimmanci musamman saboda ba lamari ba ne da ya fara faruwa yanzu, kafin sa, Janar Mahrazu Tsiga mai ritaya ya kwana fiye da kwanaki 50 a tsare bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shi a Jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa an biya kudin fansa mai yawa kafin ya samu ‘yanci. A shekarun da suka gabata, Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya ya bace yana tafiya a Jihar Filato. An gudanar da aikin bincike na tsaro kafin daga bisani a samo gawarsa a rijiya.
Idan aka duba wadannan lamuran , ba bakin cikin mutum daya ba ne, ya nuna cewa kungiyoyin masu laifi sun samu karfin zuciya har su kai hari kan mutanen da ake ganin su ne mafiya kariya da tsaro na musamman a kasar.
Idan za a iya yin garkuwa da janarori masu ritaya, a tsare su na makonni, a tilasta musu biyan kudin fansa ko su rasa rayukansu a hannun masu laifi, to sako mai tsoratarwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya da ba su da irin gogewarsu, tasirin ko karfinsu.
Yanayin ya wuce wadannan lamuran, Binciken Cibiyar Nazarin Jarida ta (ICIR) ya gano cewa akalla manyan jami’an soja 10 masu ritaya, ciki har da tsohon Shugaban Tsaro, janarori, birigediyoyi, kanar da na sama, an yi garkuwa da su ko an kashe su cikin hare-hare na tashin hankali a cikin shekaru 8 da suka gabata.
Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Tsaro, Air Chief Marshal Alex Badeh, da ‘yan bindiga suka harbe a kan hanyar Abuja-Keffi a Disamba 2018. A watan Yuni 2024, Janar Uwem Udokwere mai ritaya an kashe shi a harin da aka kai gidansa a Abuja.
Abin bakin-ciki ne cewa wasu daga cikin mutanen da sun kai matsayi mafi girma a tsarin tsaro na Najeriya yanzu sun zama wadanda abin ya shafa na rashin tsaron da suka yi rayuwarsu suna kokarin dakile shi.
Matsayin rikicin ya bayyana a cikin binciken NBS na CESPS na 2024.
Binciken ya kiyasta cewa mutane 614,937 ne aka kashe kuma aka yi garkuwa da 2,235,954 a tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024.
Ya kara kiyasta cewa an biya kusan N2.2 tiriliyan a matsayin kudin fansa a wannan lokacin, yayin da al’ummomin karkara suka fuskanci yawan kisa fiye da birane.
Haka kuma, SBM Intelligence ta ruwaito cewa akalla ‘yan Najeriya 4,722 an yi garkuwa da su tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025, kuma an biya kusan N2.57 biliyan a matsayin kuɗin fansa.
Ko da yake rahotannin biyu sun dauki lokuta daban-daban kuma sun yi amfani da hanyoyi daban-daban, duka sun yi nuni ga gaskiya daya mai damuwa ‘sace mutane ya zama daya daga cikin manyan barazanar tsaro a Najeriya’.
Bayan asarar rayuka, rashin tsaro ya haifar da babban asara a bangaren tattalin arziki. Manoma suna barin filayen noma masu albarka saboda tsoron hari.
Kasuwanci na kaura ko an rufe. Kudin sufuri da samarwa na kara hawa, yayin da masu zuba jari ke kiyaye saka hannun jari a wuraren da ba su da tsaro.
Sakamakon ba wai a al’ummomin da abin ya shafa kawai ba ne, har ma a farashin abinci, ci gaban tattalin arziki da ci gaban kasa baki daya.
Amma tambaya daya na ci gaba da damun kowa. Me ya sa kasar da sojojinta suka samu daraja ta duniya ta hanyar ayyukan zaman lafiya a Laberiya, Saliyo da sauran wurare, har yanzu take fama da mahuyacin rashin tsaro a cikin gidanta?
Daga cikin abubuwan da ke zama mai wahala shi ne rashin tsaron a yanzu babu batun iyaka da kungiya daya ko yanki daya, kasar tana fuskantar tawaye a Arewa maso Gabas, ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, rikicin kabilanci a Tsakiyarta, cibiyoyin sace mutane a jihohi da dama, da sauran ayyukan laifi.
Yawan barazanar ta sa kayayyakin aikin tsaro ya zama mai wahala samun zaman lafiya mai dorewa.
Babu shakka jami’an tsaron Najeriya sun samu nasarori masu mahimmanci kan ‘yan ta’adda da masu laifi. An kashe shugabannin ‘yan ta’adda da yawa, an rusa sansanoninsu kuma ayyuka da yawa sun tarwatsa cibiyoyin da ake aikata laifi.
Wadannan nasarorin sun cancanci a yaba musu, amma duk da haka, yawancin ‘yan Najeriya suna auna matsalar ne ta wata hanyar, ba sa yin hukunci ta hanyar amfani da kididdigar ayyuka sai abin da suke gani yau da kullum.
Suna tambaya ko za su iya tafiya ba tare da tsoro ba, ko ‘ya’yansu za su iya zuwa makaranta cikin tsaro ko kuma za su iya bacci dare daya ba tare da damuwa da hari kan al’ummarsu ba.
Daga cikin kalubalen akwai yanayin barazanar da kanta. Ba kamar yaki na yau da kullum ba, kungiyoyin masu aikata laifi a yanzu suna aiki cikin al’umma, suna dogara da masu ba da labari da ke ba da bayanai kan mutanen da za a kai hari da motsin jami’an tsaro. Suna samun abinci, man fetur da sauran kaya ta hanyar abokan wuldarsu.
A wasu lokutan, irin hare-haren da ke kai wa ba zato ba tsammani ana tsara su da bayanai da aka tattara daga mutanen da ke zaune cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Gandun dajin da ke shimfida a jihohi da dama da kuma iyakokin Najeriya manya ba tare da kulawa ba sun kara wahalar da matsalar.
Jami’an soji ka iya korar kungiyoyin daga wuri, amma saboda karancin kulawa da sarrafawa na dogon lokaci , sau da yawa suna sake taruwa a wani wuri da ban su cigaba da ayyukansu.
Dole ne al’ummomi su fuskanci gaskiya cewa kungiyoyin masu aikata laifi ba za su iya rayuwa ba tare da goyon baya daga gida ba, mutanen da ke ba da man fetur, abinci, bayanai ko mafaka ga ‘yan bindiga da masu sace mutane suna ba da gudummawa kai tsaye ga rashin tsaron da ke ci gaba da lalata al’ummomi a fadin kasar.
Haka kuma abin damuwa shi ne yanayin zargi da rashin tsaro ya haifar. Da hare-hare, a wani lokaci ake zargin kabilu baki daya a matsayin ‘yan bindiga ko ‘yan ta’addanci saboda ayyukan ‘yan laifi da wasu kalilan ke aikata.
Wannan zato ba ya karfafa tsaro, akasin haka suna raunana hadin kan kasa kuma suna karkatar da hankali daga masu aikata laifukan.
Mayar da rashin tsaro zuwa siyasa ya kara dagula lamarin. Ana fassara gazawar tsaro ta fuskar jam’iyya, yayin da ‘yan siyasa suka fi son danganta laifi maimakon gina yarjejeniya kan mafita. A halin da ake ciki, masu laifi suna ci gaba da amfani da rarrabuwa wajen fadada ayyukansu.
Watakila babbar asara ta rashin tsaron da yaki ci yaki cinyewa ita ce amincewar jama’a. Kowane sace da ta yi nasara, kowane hari kan al’umma da kowane jinkirin amsa kira na gaggawa yana raunana imanin jama’a kan ikon gwamnati na kare su. Yana nuna cewa sake gina wannan amincin daidai yake da mahimmancin da fatattakar masu laifi ke da shi.
Don haka mutuwar Manjo Janar Abubakar Rabe bai kamata ta zama kawai wani abu na bakin-ciki ba, ya kamata ya zama karin fadakarwa ga kasa baki daya.
Tambayar Najeriya a yanzu na rashin tsaro yana nan ba. Hujja ta yi yawa. Tambaya da ta bayyana ita ce ko gwamnati, jami’an tsaro, al’ummomi da ‘yan kasa sun shirya fuskantar kalubale da kwazo, hadin kai da kudurin da ya dace.
Idan janarori masu ritaya da suka shafe shekaru suna kare kasa za su zama wadanda rashin tsaro ya shafa, to ‘yan Najeriya suna da dalili na nuna damuwa.
Wannan gaskiya ita kadai ya kamata ta shaida wa kasa cewa yaki da rashin tsaro yana bukatar gaggawa fiye da kowane lokaci. Har sai haka ta faru, alƙawarin tsaro ga dukkan ‘yan Najeriya zai ci gaba da zama mafarki.












































