Gwamnatin Kano ta ayyana Talata a matsayin ranar hutu don murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar Talata 16 ga Yuni 2026, a matsayin ranar hutu domin murnar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1 ga watan Muharram 1448 bayan Hijira.

SolaceBase ta ruwaito cewa an fitar da sanarwar hutu ne cikin wasika daga Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Kano mai dauke da kwanan wata 15 ga Yuni, 2026.

A cewar wasikar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da hutun ne saboda muhimmancin kalandar Musulunci da kuma dadaddiyar al’adar Jihar Kano na murnar fara Sabuwar Shekarar Musulunci.

“Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da gobe Talata 16 ga Yuni 2026 (1 ga Muharram, 1448 Bayan Hijira), wadda ke nuni da farawar Sabuwar Shekarar Musulunci, ta zama ranar hutu ga dukkan ma’aikata a jihar,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta kuma bukaci ma’aikata da al’umma da su yi amfani da wannan dama wajen yin tunani da addu’a domin samun ci gaba, zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata a Jihar Kano da Najeriya baki daya.

Wasikar wadda Safiyya Ali Suleiman, Darakta mai kula da Gudanarwa, ya sanya wa hannu madadin Shugaban Ma’aikata.

Wannan sanarwa na nufin za a rufe ofisoshin gwamnati da cibiyoyin gwamnati a fadin jihar a ranar Talata domin baiwa ma’aikata da al’umma dama su yi bikin farawar sabuwar shekarar Musulunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here