Gwamnatin jihar Kaduna tace kimanin mutane 446 ne suka rasa rayukansu a jihar sakamakon rikicin ayyukan ta’addanci da kuma rikicin kabilanci daga watan Afrilu zuwa Satumbar shekarar nan da muke ciki.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoton tsaro na 2 da na 3 na shekarar nan ga gwamna Nasir El-Rufai, ranar Juma’a.
Aruwan, yace adadin ya kunshi mutane 285 da aka kashe a cikin watanni hudun tsakiyar shekarar da kuma 161 da suka rasa rayukansu a cikin wanni hudun karshe da muke ciki a yanzu.
Ya kuma ce an yi garkuwa da mutane 985 a tsawon lokacin da aka yi nazari a fadin jihar, inda aka yi garkuwa da 804 daga cikin adadin a zangon shekarar na uku, yayin da mutum biyar aka yi wa fyade a zango na biyu da na uku.
Kwamishinan ya ce mutane 258 ne suka samu raunuka a watanni hudun tsakiya sai 156 a watanni hudun karshe, yayin da aka yi awon gaba da dabbobi dubu 5 da 999 da kuma dubu 1 da 133 a sassan biyu, bi da bi.
Ya ci gaba da cewa, sojojin sun kashe ‘yan bindiga 168 a tsawon wannan lokaci tare da kashe 59 a watanni hudun tsakiyar Shekarar da kuma 109 a watanni hudun karshen Shekarar.
Ya yi gargadin cewa ayyukan ‘yan bindiga sun yi illa ga ayyukan noma da suka hada da kiwon dabbobi.












































