Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace wasu kadarori 40 na wucin gadi da ke da alaka da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ike Ekweremadu.
Mai shari’a Inyang Ekwo, ne ya yanke wannan hukunci a ranar juma’a, biyo bayan korafin da Ibrahim Buba, lauyan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki Tu’annati (EFCC) ya shigar.
Mista Ekweremadu da matarsa, Beatrice, a halin yanzu suna tsare a kasar Burtaniya, bisa zarginsu da safarar sassan jikin dan Adam.













































