“Herbert Wigwe ya taimake ni bayan sauke ni daga sarkin Kano” – Sanusi II

Sanusi II, Herbert Wigwe, sarkin, kano, access
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmawa a lokacin da aka sauke shi daga...

Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana yadda tsohon shugaban bankin Access, Herbert Wigwe ya ba shi gudunmawa a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulkin saraurar Kano.

Yayin da yake jawabi a taron nuna alhinin rasuwar tsohon jami’an bankin da ya rasu a wani hatsarin jirgi tare da iyalinsa a Amurka, sarkin Kanon na 14 ya ce ya kaɗu matuƙa da jin labarin rasuwar mista Wigwe wanda ya taka rawar gani a rayuwarsa.

Karin labari: Kotu ta umarci gwamnatin Kano ta biya Sarki Sanusi Miliyan 10 kuma ta bashi haƙuri

“Na yi tunanin zan riga mista Herbert rasuwa. duka mun san irin kirkinsa, da biyayyarsa,” in ji Muhammadu Sanusi ll, lokacin da yake jawabi muryarsa cike da alhini.

Ya ce tsohon jami’in bankin na Access ya yi masa alƙawarin ba shi goyon baya a lokacin da aka sauke shi daga karagar mulki.

Tsohon gwamnan CBN ɗin ya ce a lokacin har jirgin sama mista Herbert ya tanadar masa don ɗaukarsa daga Kano zuwa Legas.

Karin labari: ‘Yan sanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa a Najeriya

“A lokacin da na samu matsala a Kano, wata shida kafin a sauke ni, na kira shi na faɗa masa halin da ake ciki, sannan na ce masa, ‘Herbert na san irin ƙoƙarin da kake yi wajen magance wannan matsala, amma na san saukeni za’a yi.

“Sai ya ce mini ”mai martaba, kada ka damu. duk abin da ya faru kar ka damu muna tare da kai. A ranar da na ji sanarwa a rediyo cewa an saukeni, sai na kira shi na ce masa ina son zuwa Legas.

Karin labari: Yadda ‘yan bindiga suka kashe makiyaya da shanu 35 a jihar Filato

“An yi sanarwar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, zuwa da rana Herbert ya tanadar mini da jirgi a filin jirgin sama na Kano, sai dai a lokacin an tsara cewa za’a kaini zaman gudun hijira na shekaru masu yawa.

Daga nan sai na saka iyalina cikin jirgin tare da tura su Legas, ban yi waya da shi ba, amma ya tarbe su tare da sauke su a otal, kafin daga baya ya sama musu muhalli, inda suka kwashe watanni suna zaune kafin na komo Legas don ci gaba da zama tare da iyalaina.”

Muhammdu Sanusi ll, ya kuma ce mista Herbert ya yi masa alkawarin ɗaukar nauyin tafiye-tafiyensa bayan komawa Legas da zama.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here