Tsohon Minista Tuggar ya ki amincewa da dan takarar gwamnan APC

Ambassador Yusuf Tuggar (1)

Tsohon Ministan Harkokin Kasashen Wajen, Ambasada Yusuf Tuggar, ya sake jaddada mubaya’arsa da jajircewarsa ga jam’iyyar APC.

Ya kuma ki amincewa da ayyana tsohon Gwamna Mohammed Abubakar a matsayin dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaben 2027.

Tuggar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Mataimakinsa na yada labarai, Alkasim Abdulkadir ya fitar a ranar Alhamis a Bauchi.

Abdulkadir ya ce kungiyar yakin neman zaben Tuggar ta musanta biyayya ga Abubakar, tare da jaddada cewa babu wani zaben fidda gwani na gwamnan APC da aka gudanar bisa ka’ida a jihar.

“An ja hankalinmu kan rahotannin da ke cewa magoya bayan Ambasada Yusuf Maitama Tuggar sun amince da sakamakon zaben fidda gwani na gwamnan APC a Jihar Bauchi, kuma sun sauya sheka.

“Wannan ikirarin na karya ne kuma baya wakiltar matsayin kungiyar yakin neman zaben Tuggar ba.

“Mutanen da suka yi wa manema labarai bayani sun amince a fili cewa ba sa magana a madadin Ambasada Tuggar, kuma ba su da hurumin yin wata sanarwa a madadinsa.

“Ra’ayoyinsu nakashin kai ne kuma ba za a iya dauka cewa ra’ayin jakadan ko magoya bayansa ne ba,” in ji Abdulkadir.

Ya ce kungiyar yakin neman zaben Tuggar ta i amincewa da yarjejeniyar masalahar da aka yi, wanda ba a yi shawara da kowa ba kuma ba bisa yardar dukkan masu neman takara da manyan masu ruwa da tsaki ba.

Abdulkadir ya bukaci magoya baya da su yi watsi da wancan bayani, yana mai cewa baya wakiltar matsayin Tuggar na hukuma ba. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here