Kotu ta bai wa Jonathan damar yin takarar shugaban kasa

9010d2eb goodluck jonathan
9010d2eb goodluck jonathan

Babbar Kotun Tarayya da kea Yenegoa babban birnin jihar Bayelsa, a wani hukunci da ta yanke, ta ce tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan zai tsayawa takarar shugaban ƙasa.

BBC ta ruwaito cewa mai shari’a Isa Hamma Dashen na kotun ne ya yanke hukuncin yau Juma’a.

Haka kuma ta ruwait cewa, kawo yanzu Jonathan bai fitar da sanarwar da ke nuna cewa zai tsaya takara ba.

A kwanakin baya ne dai gamayyar kungiyoyi a arewacin Najeriya suka saya masa fom takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, sai dai tun a wancan lokaci ya ki aminta da hakan.

 

 

 

 

 

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here