Tsohon gwamnan jihar Kaduna Mmalam Nasir El-rufa’i ya ce, matukar har yanzu yana cikin gwamnatin shugaba Tinubu hakan ba zai hana shi kalubalantar tsarin gwamnatin ba, da kuma bayyana matsayarsa.
Kalaman nasa na zuwa ne a matsayin martini ga mai baiwa hugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa Daniel Bwala.
Tsohon gwamnan ya kuma koka kan tsarin dimukradiyya da ma ita kan ta jam’iyyar APCn, yana mai cewar baya bukatar kowanne irin mukami a gwamnatin Tinubu.
Cikin wani rubutu da El-rufa’I ya wallafa a shafinsa na X ya ce “Ina mayar maka da martani ne saboda ina tunanin cewa kai mai fahimta ne, amma na fadawa Tinubu karara cewa bana bukatar kowanne irin mukami a gwamnatinsa”.
Wannan dai na zuwa ne bayan da jam’iyyar APC ta caccaki El-rufa’i bayan da ta zarge shi da yunkurin janye hankalin gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC.