Garkuwa: Janar Rabe mai ritaya da matarsa sun roki a ceto su

retired Major General Rabe Abubakar former Director of Defence Information and his wife 750x430

Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) da aka yi garkuwa da shi tare da matarsa, Hajiya Amina Abubakar, sun roki gwamnati da shugabannin al’umma su shiga cikin lamarin domin a ‘yantar da su bayan sun yi mako guda a hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Katsina.

Sun yi rokon ne a wani bidiyo mai mintina 4 wanda masu garkuwar suka fitar kuma ya yadu a kafafen sada zumunta a ranar Asabar.

A cikin bidiyon, ma’auratan sun bayyana a tsaye suna magana a madadin masu garkuwar da suka nemi a sako mutane 3 da aka tsare, wadanda ake kira da Sani, Aminu da Nasiru. Haka kuma sun nemi a mayar da dabbobinsu da aka ce an kwace.

A bidiyon, Hajiya Amina ta ce masu garkuwar suna neman a sako mutanen 3, inda ta kara da cewa biyu daga cikinsu an kama su a Jikamshi yayin da na ukun aka kama shi a Kano.

“Muna rokon Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin kananan hukumomin da abin ya shafa su taimaka wajen biya musu wadannan bukatu domin mu sami ‘yancinmu,” in ji ta.

Janar Rabe, wanda ya yi magana kadan, ya roki a yi aiki don samun zaman lafiya da tattaunawa.

“Mutanen da suka rike da mu sun bayyana cewa suna son zaman lafiya tare, ina rokon duk wadanda abin ya shafa su yi aiki don samun zaman lafiya tare da tabbatar da an warware wannan matsala cikin lumana,” in ji shi.

Abin lura shi ne, ba a ambaci neman kudin fansa a bidiyon ba.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Gwamnatin Jihar Katsina da jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan bidiyon ko bukatun masu garkuwar.

An sace tsohon jami’in sojan da matarsa da direban su, Abdullahi Sa’idu, a ranar Asabar da ta gabata yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Katsina.

Shaidun gani da ido sun ce an yi wa motarsu kwanton bauna kusa da kauyen Zakin Baure, a kan hanyar Marabar Musawa Kafinsoli da ke Karamar Hukumar Matazu.

Shaidu sun ce ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin daji ne suka fito daga daga maboyarsu, tare da toshe hanya suka harbi motar lamarin da ya sa ta tsaya.

An harbi direban a hannu yayin harin amma daga baya masu garkuwar suka yi bar shi.

Majiyoyi kusa da lamarin sun ce wani shahararren jagoran ‘yan fashi, Kachallah Muhammad, ya tuntubi dangin Janar tun bayan lokacin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here