Hukumar Tsaro ta DSS ta shigar da sabbin kararrakin ta’addanci kan kwamandoji biyu na Ansaru da aka riga aka yanke musu hukunci, da sauran mambobin kungiyar 3, bisa kai hari kan makarantu a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.
An gurfanar da mutum 5 din da ake tuhuma a ranar Laraba a gaban Mai Shari’a Salim Ibrahim na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda suka musanta zarge-zarge 6 da aka shigar.
Wadanda ake tuhuma sun hada da Mahmud Muhammad, wanda ake kira Abu Bara’a ko Abbas Mukhtar, DSS ta bayyana shi a matsayin shugaban Ansaru, Abubakar Abbas wanda ake kira Isah Adam, Mahmud al-Nigeri ko Malam Mamuda, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban kungiyar kuma shugaban ma’aikata.
Sauran sun hada da Abdulrazak Umar, wanda ake kira Abu Khalifa ko Abu Khalid, Yunusa Musa Yunusa bin Musa da kuma Shamsu Adamu Sani, wanda ake kira Abu Itisar.
Sabuwar karar mai lamba FHC/ABJ/CR/438/2026 da lauyan DSS, M.E. Ernest ya shigar a ranar 29 ga Yuli, ta kunshi zarge-zarge 6 da suka shafi ta’addanci.
Wannan sabuwar karar tazo ne kwanaki kadan bayan an yanke wa wadanda ake tuhumar hukunci a wasu shari’o’i daban kan rawar da suka taka a harin.
A ranar 20 ga Yuli, Mai Shari’a Emeka Nwite na Babbar Kotun Tarayya ya yanke wa Muhammad da Abbas hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifi kan zarge-zarge 32 na ta’addanci.
Kwanaki 3 bayan haka, alkalin ya yanke wa Umar, Musa da Sani hukuncin daurin rai da rai bayan sun amsa laifin taka rawa wajen sace daliban makaranta da malamai a Karamar Hukumar Oriire.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan DSS, Calistus Eze, ya sanar da kotu cewa masu gabatar da kara sun gyara zargin domin ya hada wadanda ake tuhuma 5 duka, kuma ya nemi a karanta musu.
Lauyoyin karewa ba su yi magana ba.













































