NCAA ta fara bincikar Azman bisa zargin siyar da jirage ga kamfanin Iran

AZMAN New

 

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta fara bincike kan kamfanin Azman Air bisa zargin tura jirage biyu na Najeriya zuwa Mahan Air, wani kamfanin jiragen sama a Iran, ba tare da izini ba.

Jiragen, Airbus A340-600 (5N-AAM) da Boeing 737-300 (5N-YSM), ana zargin an tura su Iran ba tare da bin ka’idojin NCAA ba, kuma hakan ya saba wa takunkumin da Amurka da Tarayyar Turai suka kakabawa Iran.

Rahotanni sun nuna cewa jiragen suna filayen jiragen Tehran Imam Khomeini da Mehrabad, inda aka ce daya daga cikin su ya kashe na’urar bibiyar jirage yayin shiga sararin samaniyar Iran.

Daraktan Yada Labarai na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya ce hukumar za ta tuntubi takwararta ta Iran domin karin bayani kan wannan batu.

Kamfanin Azman Air ya sha fuskantar kalubale a baya, inda ya dakatar da ayyuka a 2023 da kuma 2024.

Wannan bincike ya jaddada bukatar bin ka’idojin sufurin jiragen sama da kuma takunkumin kasa da kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here