Gwamnatin jihar Kebbi ta fara shirye-shiryen daukar nauyin daurin auren ma’aurata 300 a jihar wanda aka shirya yi a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Shugaban kwamitin shirya taron, Alhaji Suleiman Argungu, ya shaida wa manema labarai ranar Lahadi a Birnin Kebbi cewa an shirya daurin auren ne da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta Nafisa Nasir Charity Development Foundation.
Ya ce an kafa kwamitoci daban-daban da ke da ayyuka na musamman kamar gwajin ciki, gwajin jini, gwajin cutar kanjamau da sauran sharuddan da suka dace na aure a jihar.
Argungu ya ce taron daurin auren ya kasance cika alkawari ne da Gwamna Nasir Idris ya yi a lokacin daurin auren da ya gabata na cewa za a gudanar da irin wadannan bukukuwan aure lokaci-lokaci domin a taimaka wa marasa galihu su yi aure.
“Gwamnatin Gwamna Idris za ta bayar da Naira 180,000 a matsayin sadaki ga kowacce amarya daga kananan hukumomin jihar 21.
“Za a samar da wasu ƙarin abubuwa kamar kayan ɗaki da kayan abinci ga duk ma’auratan don ƙarfafa dangantakar aurensu.
“Za a daura auren ne bayan tattaunawa da malaman addinin Musulunci bisa tsarin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar,” in ji Argungu. (NAN)