Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa NLC ta bayyana goyon bayanta ga umarnin da gwamnatin tarayya ta bayar na wajabta yin gwajin ƙwayoyi kafin ɗaukar aiki ga duk masu neman shiga aikin gwamnati.
Shugabar ƙungiyar kwadago ta ƙasa a jihar Legas, Funmi Sesi, ta bayyana wannan matsaya a ranar litinin yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.
Ta nuna cewa wajabta gwajin ƙwayoyi kafin ɗaukar aiki wani muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen ƙara ingancin aiki da kuma tabbatar da tsaro a wuraren aiki.
Ta bayyana cewa manufar za ta taimaka wajen magance matsalar yawaitar amfani da miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa da manya, wadda ta jawo koma baya ga ingancin aiki, lafiyar ma’aikata da kuma ƙwarewar aiki a ƙungiyoyi da dama.
Karanta: Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya faɗi
Shugabar ta jaddada cewa shan ƙwayoyi na da tasiri kai tsaye ga aikin ma’aikata da ƙwazonsu, don haka ya dace masu ɗaukar aiki su tabbatar da cewa waɗanda ake ɗauka cikin aikin gwamnati suna da cikakkiyar lafiya da cancanta.
Ta kuma yi nuni da cewa irin wannan tsarin gwajin ƙwayoyi ya riga ya kasance a manyan makarantu, inda ake tantance ɗalibai kafin karɓar su karatu, tare da cewa faɗaɗa tsarin zuwa fannin daukar aiki zai ƙarfafa ɗa’a da alhakin aiki.
Sai dai ta yi gargaɗi kan yiwuwar amfani da manufar ta hanyar da ba ta dace ba, tana nuna buƙatar aiwatar da tsarin cikin gaskiya, adalci da kuma kare haƙƙin masu neman aiki, domin kauce wa son kai ko cutarwa daga wasu jami’ai.












































