Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya yaba wa wani malami dan asalin Ilorin kuma ma’aikacin yada labarai, Dokta Daud Awwal, bisa gudunmawar da ya bayar ga ilimin Musulunci ta hanyar fassarar Alkur’ani mai girma zuwa manyan harsuna biyu.
Sarkin ya bayyana haka ne yayin da ya karbi Awwal a fadarsa da ke Ilorin Jihar Kwara. Awwal ya mika masa kwafin sabon aikinsa da ya kammala mai suna Cikakkiyar Fassara ta Alkur’ani Mai Girma daga Larabci zuwa Yarbanci da Turanci, tare da sigar fassarar da aka tsara domin taimaka wa wadanda ba sa iya karatun Alkur’ani daidai ga Sarkin.
Sulu-Gambari ya bayyana Awwal a matsayin jakada nagari na Masarautar Ilorin kuma fitaccen memba na al’ummar Najeriya mazauna kasashen waje a Birtaniya.
Ya yaba wa Awwal kan jajircewarsa wajen inganta ilimi, kyawawan dabi’u da ilimin addini duk da cewa yana da yawan aiki a kasashen waje.
“Wannan babban nasara ce wadda za ta taimaka sosai wajen kiyaye al’adun Musulunci na Masarautar Ilorin, tare da saukaka isar da sakon Allah na Alkur’ani Mai Girma ga jama’a sosai, musamman mutanenmu da suka fi iya Yarbanci da Turanci,” in ji Sarkin.
Tun da fari, Dokta Daud Awwal ya bayyana godiyarsa ga Sarkin bisa jagoranci da goyon bayansa mara iyaka ga malaman addini.
Ya bayyana cewa abin da ya sa shi fara wannan aiki shi ne don cike gibin rashin fahimtar harshe, da kuma baiwa Musulmai masu jin Yarbanci da Turanci damar fahimta, karantawa da yin tunani kan koyarwar Alkur’ani Mai Girma.
Awwal ya kara da cewa an tsara sashen fassarar ta Alkur’ani Mai Girma ne musamman don taimaka wa wadanda ba sa iya karanta rubutun Larabci amma suna son karanta Alkur’ani da furtawa daidai.













































