Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar, ya warware rikicin da ya kai ga dakatar da shugaban karamar hukumar Yankwashi Mubarak Ahmad.
Tun da fari dai majalisar dokokin jihar Jigawan ce ta dakatar da Mubarak Ahmad, bayan samun takardar korafi daga jam’iyyar APCin jihar bisa zarginsa da rashin yin biyayya, ga na sama da shi a jam’iyyance.
Sai dai gwamnan jihar Jigawa ya bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su yi hakuri tare kuma da bada umarnin mayar da shugaban karamar hukumar kan kujerarsa.













































