Gwamnatin Kano ta ayyana 1 ga Satumba a matsayin ranar hutun zuwa aiki

Abba Kabir Yusuf 680x430

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Talata, 1 ga Satumba 2026, a matsayin rana hutun zuwa aiki domin baiwa mazauna jihar damar murnar bikin Takutaha, wani bikin addini na gargajiya da ake gudanarwa duk shekara a fadin jihar.

An bayyana hakan ne cikin Takardar Tsarin Aiki mai Lamba 7/2026 da Babban Sakataren a Hukumar Ma’aikata, Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikata.

A cewar takardar, rana hutun zuwa aiki ta yi daidai da 19 ga watan Rabi’ul Awwal, 1448AH, kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya amince da ita.

Gwamnatin ta bayyana Takutaha a matsayin muhimmiyar dama ta addini wadda ke da zurfin ma’ana ta ruhaniya da al’ada ga al’ummar Kano, inda ta ce tana daga cikin gadon Musulunci na jihar.

Ta bukaci ma’aikatan gwamnati da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’a, tunani, musamman domin neman albarkar Allah don ci gaba da samun zaman lafiya, hadin kai, kwanciyar hankali da wadata a Jihar Kano da Najeriya baki daya.

SolaceBase ta ruwaito cewa takardar ta umurci shugabannin ma’aikatu, sassa da hukumomi da su tabbatar an bi wannan umarni.

Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa ayyukan gaggawa za su ci gaba bisa ka’idojin da aka saba.

An tura takardar zuwa ga manyan jami’an gwamnati ciki har da Shugaban Ma’aikata, Sakataren Gwamnatin Jihar, kwamishinoni, Sakatarori, Shugabannin hukumar, Masu sa ido kan kananan hukumomi, da Shugabanin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here