An kama dan basajan shugaban hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa a Abuja

Hudu Salman Umar
Hudu Salman Umar

Hukumar dake yaki da cin-hanci da rashawa a Najeriya (EFCC) ta kama wani dan basaja mai suna Umar Hudu, mai shekaru 38, wanda dan asalin jihar Kano ne.

Kamar yadda hukumar ta ce, an kama Hudu ne a wani hotal dake babban barnin tarayya Abuja, ya yin da yake bayyana kansa a matsayin shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo ranar Talata.

Ana zargin Haladu da karbar Naira 100,000 daga hannun wani mutum da niyar zai taimakamsa a kan wani lamari da ya shafi hukumar ta EFCC.

Hukumar ta kara da cewa wanda ake zargi ya bada cikaken bayanai, kuma za’a gurfanar dashi a kotu domin girbar abinda ya shuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here