By Fatima Maje
Sarkin Kano na goma sha daya, Khalifah Muhammadu Sanusi II, ya ce ya zo Kano ne saboda rashin yanayi mai kyau wanda ya hana jirginsa wucewa zuwa Jihar Jigawa, hakan ya sa dole ya tsaya a kano.
“Ba zan iya wucewa zuwa Jigawa ba saboda rashan yanayi mai kyau, hakan ya sa dole mu tsaya a Kano, mutanan da suka tarbe ni suka nemi na je na gaishe da mahaifiya ta.” Inji Khalifa Sanusi.
Khalifan ya kuma tunawa jama’a cewa duk dan Najeriya na da ‘yan cin zuwa duk inda yake so.
Jaridar Solacebase ta rawaitu cewa wannan shine zuwan sa Kano na farko, bayan shekaru uku da cireshi daga sarkin kano da gwamna Abdullahi Ganduje ya yi.













































