Mutane bakwai sun mutu, yayin da guguwa da ruwan sama mai karfi suka shafi wasu mazauna 5,403 a Jihar Jigawa.
Sakataren Zartarwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA), Hannafi Yakubu ne ya tabbatar da mutuwar ga manema labarai a Dutse ranar Laraba.
Ya ce bala’in ya shafi garuruwa 120 a Kananan Hukumomi 13 na jihar, inda ya shafi makarantun gwamnati 47, cibiyoyin kiwon lafiya 3 da gidajen ‘yan sanda 2.
Yakubu ya ce hukumar ta tattara bayanai kan wadanda bala’in ya rutsa da su da kuma dukiyoyin da ta lalata tun daga farkon lokacin damina har zuwa yau.
Kananan Hukumomin da abin ya shafa sun hada da Dutse, Gwaram, Birnin Kudu, Kiyawa, Babura, Gumel, Kaugama, Ringim, Gagarawa, Kirikasamma, Suletankarkar, Miga da Buji.
Sakataren ya ce gwamnatin jihar ta raba kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu radadin da suke ciki.
Yayin da ya yi kira ga masu bada taimako a cikin jama’a, masu kudi, kungiyoyi da hukumomin agaji da su taimaki wadanda abin ya shafa, Idan ya sake jaddada aniyar gwamnati na kare al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali ta hanyar daukar matakan agajin gaggawa.
“Bala’i na shafan kowa ne, don haka dole ne su taimaka wajen magance matsalar.
“SEMA, tare da goyon bayan gwamnatin jihar, na shirye don taimaka wa wadanda abin ya shafa duk lokacin da bala’i ya faru,” in ji shi. (NAN)













































