Ɗan Atiku ya fice daga PDP zuwa APC, tare da nuna goyon baya ga Tinubu

Atiku sad sad

Abubakar Atiku Abubakar, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki, tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Abubakar Atiku Abubakar, wanda aka fi sani da Abba, an tarɓe shi a hukumance a Majalisar Tarayya da ke Abuja, inda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da manyan jiga-jigan APC daga Arewa maso Gabas suka karɓe shi, lamarin da shugabannin jam’iyyar suka bayyana a matsayin babban ƙari ga ƙoƙarin APC na ƙarfafa matsayinta gabanin zaɓe.

A yayin sanar da sauya sheƙarsa, Abba ya fice daga PDP tare da yanke shawarar rungumar APC gaba ɗaya, yana bayyana wannan mataki a matsayin kashin kai kuma mai muhimmancin tarihi.

Ya kuma umarci mambobi da masu jagorancin ƙungiyarsa ta siyasa, wadda aka sani da Haske Atiku Organisation, da su shiga APC nan take domin aiki da tallata ajandar sabunta manufa ta Shugaba Tinubu.

Abba ya danganta wannan shawara da salon jagoranci da halayen siyasa na Sanata Barau Jibrin, inda ya yaba da rawar da yake takawa a siyasar ƙasa.

Ya kuma ce, zai yi aiki tare da Sanata Barau domin tabbatar da nasarar neman wa’adi na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Da yake maraba da sauya sheƙar, Mataimakin Shugaban APC na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Kwamared Mustapha Salihu, ya bayyana lamarin a matsayin alamar faɗaɗar tasiri, yana nuna siyasa mara shinge, tare da cewa matasan ‘yan siyasa na karkata ga manufofi da shirye-shirye fiye da tsofaffin rabuwar siyasa.

A nasa ɓangaren, Sanata Barau Jibrin ya taya Abba murna bisa abin da ya kira mataki mai jarumta da nagarta, yana mai cewa sauya sheƙar ta samo asali ne daga amincewa da jagorancin Shugaba Tinubu da ajandar sabunta manufa, ba tasirin iyali ba.

Taron ya kuma shaida sauya sunan ƙungiyar siyasar Abba daga Haske Atiku Organisation zuwa Haske Bola Tinubu Organisation, alamar cikakken sauyin alkiblar siyasa gabanin zaɓen gama gari na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here