Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da hare-haren ‘yan bindiga da aka ruwaito a Kananan Hukumomi 4 na jihar, tare da tabbatar wa al’ummar da abin ya shafa cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
SolaceBase ta ruwaito cewa yankunan da abin ya shafa sun hada da Chiromawa a Karamar Hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji da wasu al’ummomi da ke kewayen Karamar Hukumar Gwarzo.
Gwamna Yusuf ya yi ta’aziyya ga wadanda abin ya shafa da iyalan su, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.
Ya tabbatar wa al’ummar da abin ya shafa cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace, tare da hadin gwiwar jami’an tsaro, domin hana sake faruwar hare-hare da dawo da kwarin gwiwa ga mazauna yankunan.
Gwamnan ya ce an ba da umarni ga hukumomin da suka dace su karfafa sa ido, tattara bayanan sirri da tsarin daukar mataki cikin gaggawa a yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma bukaci mazauna yankuna su kwantar da hankula su kuma guji duk wani abu da zai kara dagula lamarin, ya kuma tabbatar musu cewa gwamnati na aiki tare da jami’an tsaro domin magance matsalar.
Gwamna Yusuf ya kara yin kira ga jama’a su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar ba da sahihan bayanai da za su taimaka wajen hana sake faruwar hare-hare da kuma kama ‘yan ta’addan.
Ya yaba wa kokarin jami’an tsaro kuma ya bukace su ci gaba da gudanar da ayyuka bisa bayanai domin kare al’ummar da ke cikin hadari a fadin jihar.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa da kuma dawo da duk wanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.
Ya sake nanata kudurin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin dukkan mazauna jihar, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Jihar Kano.












































