Hadakar jami’an tsaro sun tare hanyar shiga fadar Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Laraba.
SolaceBase ta tattaro cewa wani faifan bidiyo a daren ranar Talata ya bayyana cewa wasu matasa na shirin kai hari a fadar sarkin Nasarawa a safiyar ranar Laraba domin korar Sarkin Kano na 15.
A cikin faifan bidiyon, an bukaci magoya bayan sarkin Kano na 15 su ma su fito domin kare fadar.
Majiya mai tushe ta shaida wa SolaceBase cewa wasu daga cikin matasan da aka kama suna dauke da muggan makamai.
Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro a kewayen fadar Sarkin Nasarawa tare da mayar da titin hannu daya.
Karin karatu: Hukumar kiyaye hadurra ta FRSC ta kaddamar da sabbin dabarun dakile hadarurruka da ake yi a kan tituna
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce an samar da isassun matakan tsaro domin dakile duk wani abu da zai iya haifar da karya doka da oda a jihar.
Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan sahihan rahotannin sirri na wani shirin yin kazamar zanga-zangar da wasu mutane ke shirin yi, wanda ya sa rundunar ‘yan sandan tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro suka baza jami’ansh da zuwa wasu muhimman wurare a cikin babban birnin Kano domin hana zanga-zangar da kuma tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.
A cewar sanarwar, sakamakon wadannan matakan da aka dauka, an kama wasu mutane 17 da ake zargi da aikata laifuka, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.